Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Mali ce ta sanar da hakan a cikin wani bayani da ta fitar a jiya, inda ta tabbatar da cewa an samu kwayoyin cutar na Ebola ne a jikin yariyar wadda shekarunta na haihuwa ba su biyu ba, kuma tana tare da kakarta, amma tuni aka killace yarinyar, haka nan kuma dukkanin mutane da suke tare da ita ana gudanar da bincike a kansu.
A cikin watan Afirilun da ya gabata an yi shakku kan wasu mutane kan ko suna dauke da kwayoyin cutar a kasar Mali, amma daga bisani bincike ya tabbatar da cewa ba su dauke da kwayoyin cutar. A ranar 20 ga wannan wata ne dai hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar da cewa a halin yanzu babu wani mutum da ke dauke da kwayoyin cutar ta Ebola a Najeriya. ABNA